fidelitybank

Masarautar Katsina ta janye sarautar da ta baiwa Saddiq Musa Kaita

Date:

Masarautar Katsina da ke Arewacin Najeriya ta dakatar da sarautar Sardaunan Katsina da aka bai wa Saddiq Musa Kaita.

Wata sanarwa da Alhaji Sule Mamman Dee, Sarkin Tsaftan Katsina ya sanya wa hannu ta ce nan gaba za a tuntube shi domin yi masa karin bayani.

“Bisa ga takardar da aka ba ka ta ranar 16/4/2022 wadda aka ba ka Sarautar Sardaunan Katsina, Majalisar Mai martaba Sarkin Katsina ta umarce ni da na rubuto na sanar da kai cewa ta dakatar da Sarautar.

Komi ke nan za a tuntube ka nan gaba,” in ji sanarwar.

Tun da farko farko Sarkin Katsina ya tabbatar masa da sarautar ne a cikin wata takarda mai É—auke da sa hannunsa a ranar Asabar 16 ga watan Afrilu.

“Na amince da ba ka Sarautar Sardaunan Katsina kamar yadda ka nema,” kamar yadda Sarkin Katsina ya bayyana a cikin takardar.

Sanarwar ta ce nan gaba za a sanar da ranar bikin naÉ—in nasa.

Saddik jika ne ta bangaren uba ga sarkin Fadan Katsina Isma’ila Damale wanda shi kuma ɗa ne ga Wazirin Katsina na farko Haruna Kaita.

Haka kuma ta bangaren uwa jika ne ga Makaman Katsina Marigayi Tukur Idris Nadabo hakimin Bakori.

A kwanakin baya ne aka ba Ibrahim Ida sarautar Wazirin Katsina wanda a baya shi ne Sardaunan Katsina.

Wannan na zuwa ne bayan ajiye sarautar waziri da Alhaji Sani Lugga ya yi saboda wasu dalilai.

latest news in nigeria 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp