Majalisar Masarautar Katsina ta sanar da dakatar da Durbar a lokacin bukukuwan Eid-el-Kabir a ranar Asabar.
Sanarwar dakatarwar ta fito ne a wata sanarwa da ta fitar jiya a Katsina, ta hannun mataimakin sakataren majalisar, Sule Mamman-Dee.
Ya ce, dakatarwar ta biyo bayan yanayin tsaro da ake fama da shi a jihar.
A cewar Mamman-Dee, Sarkin, Abdulmumini Kabir-Usman, ya nuna matukar damuwarsa kan matsalar tsaro a sassan masarautar, inda ya ce zai halarci Sallar Idi ne kawai a ranar Asabar.
Ya bayyana cewa, Sarkin ya shawarci al’ummar Musulmi da su ci gaba da yin addu’o’in samun zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.
Bikin Durbar dai ya samo asali ne tun shekaru aru aru, kuma ya kunshi baje kolin fasahar hawan doki daga gundumomi da masu fada aji, wadanda suke yiwa Sarkin Mubaya’a a ranar Idi, wanda aka fi sani da ‘Hawan Daushe’ a Katsina.
A nasa bangaren, Sarkin ya jagoranci tawagar ‘yan majalisar Masarautu da hakimai da kauye a cikin jerin gwanon dawaki da aka fi sani da ‘Hawan Bariki’ domin yin mubaya’a ga gwamnan jihar, kwana guda bayan kammala Idi.
Hakazalika kakakin masarautar Daura a jihar, Usman Ibrahim ya ce majalisar ta kuma dakatar da gudanar da bukukuwan Sallah a fadin masarautar.
A cewar Ibrahim, Sarkin, Faruk Umar-Faruk ya umurci dukkanin hakimai da ke karkashin masarautar su gudanar da Sallar Idi-El Kabir a yankunansu.
Ibrahim ya ce, Sarkin ya kuma yi kira ga maniyyatan da ke zuwa aikin Hajji da su yi addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da kasa baki daya.