An buɗe mashigin kan iyakar Rafah da ke tsakanin Gaza da Masar domin kai kayan agaji ga dubban fararen hul.
An ga manyan motoci ɗauke da kayan agaji na shiga ta kan iyakar daga Masar zuwa Gaza.
Kawo yanzu ba a san tsawon wane lokaci mashigin zai ɗauka a buɗe ba.
Isra’ila ta amince da barin manyan motocin 20 shiga zuwa Gaza.
Majalisar Dinkin Duniya ce ta yi kiran buɗe kan iyakar domin isar da kayan agaji ga fararen hular da cikin tananin buƙatar tallafin.


