Masar da Isra’ila da Tarayyar Turai sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta fitar da iskar gas.
An cimma wannan yarjejeniya a yayin wani taro da aka yi a wani taro kan makamashi a Cairo.
A yayin taron, an fi mayar da hankali ne kan yadda Tarayyar Turai za ta rage dogaro da gas ɗin Rasha.
Ana sa ran gas ɗin da Isra’ila ke samarwa za a tura shi a ta ce shi a Masar, inda daga nan za a saka shi a jirgin ruwa zuwa Turai.
Ma’aikatar makamashi ta Isra’ila ta bayyana cewa a karon farko, za ta bari a fitar da gas ɗinta mai yawa zuwa ƙasashen Turai. In ji BBC.