Guda daga cikin jarumi a masana’antar Kannywood, Nuhu Abdullahi, ya mayar da martani mai zafi ga Sarkin waka, Naziru, kan batun danne hakkin wasu daga cikin jarumai da a ke yi musu a cikin masana’antar.
A wata hirar da BBC da wata tsohuwa kuma jarumar Kannywood, Ladi Cima, ta yi na farke laya da ta yi a kan danne mata hakki ya jawo mabudar kofar tofa albarkacin wasu daga cikin ‘yan masana’antar.
Mawaki Naziru Sarkin Waka ya yi fashin baki sosai a kan haka, kuma da alama ya goyi bayan hirar Ladin Cima, kan rashin biyan hakkin aiki yadda ya kamata ga Jarumai.
To sai dai a nasa kalaman, Jarumi Nuhu Abdullahi, ya yi masa raddi, inda ya ke sukar Naziru da cewar ya fara yi wa ‘yayan sa, Aminu Saira wa’azi game da biyan hakkin kudin ma’aikata kafin yazo ya ce, wani abu.