Shugaban kungiyar marubuta wasanni ta kasa (SWAN), reshen jihar Bauchi, Mahmud Yakubu Muhammad ya ce, kwararrun ‘yan jarida su kasance wajen bayar da rahotannin wasanni a jihar.
Ya bayar da wannan shawarar ne a ranar Litinin din da ta gabata yayin bikin bude makon SWAN na Bauchi 2022 wanda aka gudanar a cibiyar ‘yan jarida ta NUJ Bauchi.
A cewarsa, manufar makon SWAN ita ce kulla kyakkyawar alaka a tsakanin masu aikin yada labarai ta hanyar wasanni, inda ya kara da cewa, makon kuma wata hanya ce ta samar da ingantacciyar gasa ta wasanni daban-daban da za a yi a cikin mako.
Ya ce, kungiyar za ta shirya horas da marubutan wasanni a jihar domin su fadakar da su yadda ake tafiyar da harkokin wasanni tare da kara kaimi wajen bayar da rahotanni a wasanni.
Shugaban SWAN ya bayyana cewa, ya kamata ‘yan jarida su rika motsa jiki a ko da yaushe domin su kasance cikin koshin lafiya domin yana inganta lafiyar jikin mutane da kuma inganta lafiyar kwakwalwa da tunani.
“Lafiyar mambobinmu da ta sauran ‘yan jarida na da matukar muhimmanci, don haka akwai bukatar su kasance masu dacewa da hankali. Ta hanyar wasanni, za su ci gaba da kasancewa cikin koshin lafiya, ta yadda za su yi aiki mafi kyau a ayyukansu a matsayin masu aikin watsa labarai, ”in ji shi
Shima da yake jawabi, shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ), majalisar jihar Bauchi, Kwamared Umar Sa’idu, ya ce wasanni ba wasa ba ne na nishadantarwa ko kasuwanci, illa dai karfi ne da ke hada kan ‘yan Najeriya.
Ya yabawa kungiyoyin yada labarai na jihar kan yadda suke bunkasa harkokin wasanni ta hanyar rahotannin da suke bayarwa tare da karfafa musu gwiwa su ci gaba da gudanar da ayyukansu.