Marseille ta kulla yarjejeniya da tsohon kocin Brighton, Roberto De Zerbi, domin ya zama sabon kocinta.
Kungiyar ta Ligue 1 ta sanar da hakan a ranar Litinin.
Marseille ta lura da cewa “suna aiki tare da duk bangarorin da abin ya shafa don tsara zuwan kocin Italiya da ma’aikatansa a kan benci na OM, da kuma shirya zuwansa Marseille a cikin kwanaki masu zuwa.”
De Zerbi ya jagoranci Brighton zuwa matsayi na shida a gasar Premier a kakar 2022/2023.
A yin haka, ya taimaka wa Seagulls samun cancantar shiga gasar Turai a karon farko a tarihinsu.
Daga karshe Roma ta fitar da su a gasar cin kofin Europa League zagaye na 16.
Brighton ta kare a matsayi na 11 a kakar wasan data gabata kuma De Zerbi da kungiyar sun yanke shawarar rabuwa.