Fitaccen jarumin nan dan kasar Amurka, Jaden Smith, ya jinjinawa mahaifinsa, Will Smith, bayan da ya mari fuskar dan wasan barkwanci Chris Rock, saboda yin ba’a game da mahaifiyarsa Jada Pinkett-Smith a wajen bikin bayar da lambar yabo ta Oscars da aka kammala kwanan nan a ranar Lahadi, 27 ga Maris.
Ripples Nigeria ta rawaito cewa, fitaccen jarumin nan Will Smith ya mari fuskar Rock a dandalin Oscars bayan ya yi wa matar sa ba’a.
Wani fitaccen jaeumi Smith, ya tsawatar da dan wasan barkwanci, bayan ya mari fuskarsa. Ya gaya wa Chris Rock kada ya taba yin wasa da matarsa.
Da yake mayar da martani kan lamarin, Jaden ya rubuta a dandalinsa na Twitter, “Kuma haka muke yi.”