Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya tunatar da mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero cewa mahaifinsa, Alhaji Ado Bayero, ya shaida musu a wata ziyara da ya kai fadar cewa shi (Atiku) zai zama shugaban kasa.
“Mun kai ziyarar ban girma zuwa fadar a wani lokaci a lokacin da nake Mataimakin Shugaban Najeriya, sai marigayi Sarki Ado Bayero ya ce a cikinmu ya ga wani da zai zama Shugaban kasa wanda zai kawo wa Najeriya girma.” Inji Atiku.
Atiku Abubakar ya kara da cewa marigayi sarki Ado Bayero bai tsaya a haka ba. Ya kuma ci gaba da addu’ar Allah ya baiwa shugaban kasar da ya gani ya kawo wa Nijeriya hayyacinta, ya kuma inganta zamantakewa da tattalin arzikinta.
Karanta Wannan: Kotu ta hana Wike kama magoya bayan Atiku
Ya ce, ya yi imanin cewa shi ne wanda Marigayi Sarki Ado Bayero ya ambata shi ya sa ya zama wajibi mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi koyi da shi tare da yi masa addu’a domin cimma burin Marigayi Bayero.
Atiku Abubakar, wanda ke Kano a kan yakin neman zabensa na shugaban kasa, ya kasance a fadar sarkin kasar a ziyarar ban girma, tare da mukarrabansa, ciki har da dan takarar mataimakinsa Ifeanyi Okowa.