Hukumar ƙididdiga ta ƙasa ta ce, an samu ƙari kan yawan mutanen da ba su da aikin yi zuwa kashi 4.2 cikin 100 a cikin watanni shida na farkon shekarar 2023 daga kashi 4.1 cikin 100 a watanni ukun farko na shekarar nan.
NBS ta bayyana haka ne a alƙaluman da ta fitar game da yanayin ayyukan yi a bana.
A cewar hukumar, rashin aikin yi a tsakanin maza ya kai kashi 3.5 cikin 100 yayin da a ɓangaren mata ya kai kashi 5.9 cikin 100 a watanni shidan farko na 2023.
Rahoton ya kuma nuna cewa a tsukin watanni shidan na farko, yawan masu aikin da bai kai su biya buƙatunsu ba ya kai kashi 11.8 cikin 100, inda alƙaluman ya yi ƙasa daga kashi 12.2 cikin 100 na watanni ukun farko na 2023.
“Game da alƙaluman matasa masu aikin yi ƴan tsakanin shekara 15-24 ya kai kashi 7.2 cikin 100 a tsukin wata shidan farko na bana.


