fidelitybank

Manyan ‘yan siyasa da shugaban kasar Taiwan za su bayar da albashin su ga Ukraine

Date:

Shugabannin siyasa na Taiwan haɗi da Shugabar kasar, Tsai Ing-wen, za su bayar da albashinsu na wata daya, domin tallafa wa mutanen da suke tserewa daga yakin Ukraine.

Mataimakin shugabar kasar da firimiya da kuma shugabannin ‘yan hamayya na daga cikin wadanda suka yi alkawarin ba da albashinsu.

Shugaba Tsai ta ce tana fatan dukkanin alummar Taiwan da ma’aikatan gwamnati za su taimaka wa al’ummar ta Ukraine.

Ta ce: ”Ma’aikatar Harkokin Waje za ta sanar da kafa asusun banki na musamman domin tattara tallafin na Ukraine, wanda hukumar ba da tallafin gaggawa ta samar. Hatta daidaikun jama’ar kasar ta Taiwan an bukace su da su ba da tallafin.”

Bayan tallafin kudi da za ta bayar, gwamnatin Japan tana kuma shirin aikawa da taimakon kayayyakin kula da lafiya domin ‘yan gudun hijirar na Ukraine.

Taiwan na nuna goyon bayanta ga Ukraine, saboda ita ma tana fuskantar irin wannan barazana ta mamaya daga China, wadda ke ikirarin tsibirin nata ne. In ji BBC.

nigerian news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp