fidelitybank

Manyan Sojoji su yi ritayar dole zuwa ranar Litinin – Rundunar Soji

Date:

Shalkwatar tsaro, ta umarci manyan sojoji da suka haura kwas na 39 a makarantar horas da manyan sojoji da su ajiye aiki bisa raɗin kansu.

Matakin na zuwa ne bayan da Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sabbin hafsoshin tsaron ƙasa.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar mai ɗauke da sa hannun Manjo janar Y. Yahaya a madadin babban hafsan tsaron ƙasar.

“An umarce ni na buƙaci duka manyan sojoji da ke sama da kwas na 39 na makarantar horas da manyan hafsoshin sojin ƙasar, su gaggauta miƙa takardun ajiye aiki bisa raɗin kai”, in ji sanarwar.

“Haka kuma ana buƙatar waɗanda umarnin ya shafa su mika takardun nasu ga shalkwatocin tsaron da suke aiki zuwa ranar Litinin 3 ga watan Yulin 2023”.

Bisa ga al’adar aikin soji, manyan jami’ai ba za su karɓi umarni daga sojojin da suka girma a aiki ba.

Dan haka naɗin sabbin manyan hafsoshin tsaron da shugaban ƙasar ya yi, zai tilasta wa manyan sojoji kusan 100 ajiye aikinsu.

Waɗanda suka haɗar da Janar-janar, da masu muƙamin Burgediya janar da masu muƙamin Air Vice Marshal da muƙamin Admirals a rundunonin sojin ruwa da na sama.

Shi dai sabon babban hafsan tsaron ƙasar Manjo Janar Christopher Musa ɗan kwas na 38 ne na makarantar horar da manyan hafsoshin tsaro, yayin da sauran manyan hafsoshin sojin ƙasa na sama da na ruwa su kuma ‘yan kwas na 39 ne.

bbc news nigeria today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp