fidelitybank

Manyan kungiyoyi na zawarcin Osimhen – Mai horas da Najeriya

Date:

Kocin Super Eagles, Jose Peseiro, ya bayyana dalilan da yasa manyan kungiyoyi kamar Chelsea, Manchester United, Real Madrid da Tottenham Hotspur ke zawarcin Victor Osimhen.

Osimhen ya zama abin labari, saboda bajintar da ya ci tun lokacin da ya koma Napoli daga kulob din Lille 1 a 2020.

A kakar wasa ta bana, dan wasan mai shekaru 23 ya zura kwallaye tara a wasanni 13 da ya buga a Napoli.

A halin yanzu Osimhen yana daya daga cikin ‘yan wasan gaba da ake nema ruwa a jallo a duniya a halin yanzu.

Peseiro ya bayyana cewa babu wata kungiya a duniya da zata wuce daman samun Osimhen a kungiyar saboda halayensa.

“Yana zura kwallaye da yawa kuma matashi ne. Tabbas ba abu ne mai sauki ba, yawanci dan wasan gaba yana samun wannan matakin daga baya,” Peseiro ya fada wa gidan yanar gizon Italiyanci, Tuttomercatoweb.

“Amma yakan zira kwallaye a raga, a wannan lokacin, bana jin banyi kuskure ba idan nace kowace kungiya a duniya tana son siyan shi.

“Ya san yadda ake dannawa, ya san yadda ake zura kwallo, ya san yadda ake amfani da jikinsa. Zai san yadda ake buga wasa a dukkan kungiyoyi.”

Ana sa ran za a saka sunan Osimhen a cikin ‘yan wasan Najeriya da za su buga wasan sada zumunta da Portugal.

sun news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp