An dage taron da manyan hafsoshin sojin Afirka ta Yamma da suka shirya yi don tattauna batun juyin mulkin Nijar.
Tun farko an sa ran taron, wanda kungiyar Ecowas mai raya tattalin arzikin ƙasashen na Afirka ta Yamma ta kira, za a yi shi ne a Accra, babban birnin kasar Ghana a yau Asabar.
Babu wani dalili da aka bayar game da daga taron.
A ranar Alhamis Ecowas ta bayar da umarnin cewa dakarun kungiyar su kasance cikin shiri don dawo da mulkin farar hula a Nijar.
Shugaban mulkin soja Abdourahmane Tchiani, wanda ya ƙwace mulki ranar 26 ga watan Yuli, ya kafe cewa duk ƙasar da ta kai musu hari za su kare kansu