Manyan ƴan jam’iyyar Democrats a Amurka na ci gaba da nuna goyon bayansu ga mataimakiyar shugaban kasar a matsayin ƴantakara bayan janyewar shugaba Biden a takarar zaɓen watan Nuwamba.
Gwamnan jihar Carlifonia Gavin Newsom ɗaya daga cikin wadanda ake ganin za su fito su kalubalance ta ya sanar da mara mata baya, yana mai bayyana ta a matsayin marar tsoro.
Tun farko dai Harris ta gode wa goyon bayan da shugaba Biden ya ba ta, inda ta bayyana matakinsa na janyewa a matsayin kishin ƙasa da rashin fifita bukatun kashin kai.
Tuni gwamnoni uku, da sanatoci takwas da gwamman ‘yan majalisar wakilai suka sanar da goya mata baya.
Hakama tsohon shugaban ƙasar Bill Clinton da matarsa Hillary Clinton da wasu mashahuran ‘yan fim da mawaka na Hollywood sun ce suna tare da ita.


