fidelitybank

Manoman shinkafa a Kano 40,000 ne za su ci gajiyar gwamnatin tarayya

Date:

Akalla manoman shinkafa 40,000 ne a jihar Kano za su ci gajiyar shirin gwamnatin tarayya na Anchor Borrower Programme (ABP), domin habaka noman shinkafa.

Shugaban kungiyar manoma shinkafa ta kasa (RIFAN) na jihar, Alhaji Abubakar Aliyu ne ya bayyana hakan, a wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranar Lahadi a Kano.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa, ABP wani muhimmin bangare ne na manufar sauya fasalin noma na gwamnatin tarayya da aka tsara, don bunkasa hanyoyin samar da kayan amfanin gona, samar da kudaden noma, karfafa dabarun kasuwancin manoma, kara darajar da samar da kasuwa ga amfanin gona.

A na aiwatar da ABP ne tare da haɗin gwiwar Babban Bankin Najeriya (CBN), ƙungiyoyin bankunan kasuwanci da gwamnatocin jahohi ta hanyar dillalan noma da ake kira “anchor clients.”

Aliyu ya ce, shirin zai samar da takin zamani da kayan masarufi ga masu noman shinkafa 15,000 a lokacin noman rani yayin da wasu 25,000 kuma za a tallafa musu a lokacin noman 2022.

“Amma, ba mu shiga noman bana ba saboda wasu matsaloli tsakanin CBN da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi.

Gwamnati ta yanke shawarar mayar da manoma 40,000 da aka yi niyya zuwa damina, ya danganta da yadda al’amura ke gudana,” inji shi.

sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp