Manoman jihar Borno sun gudanar da addu’o’i na musamman, saboda rashin samun ruwan sama.
Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa NAN ya ruwaito cewa, manoman da galibinsu a yankunan arewaci da tsakiyar jihar da ci gaban ya shafa sun koma yin addu’o’in neman taimakon Allah.
Manoman da dama a kananan hukumomin Maiduguri, Jere, Konduga, Kaga da Mafa sun ce ci gaban ya tayar da hankali kuma suna bukatar addu’a.
“Za ku ga gajimare kamar za a yi ruwan sama amma bayan wani lokaci za a yi iska mai ƙarfi tana tura gajimaren zuwa wani wuri kuma ƙarshen ke nan.
“Idan abubuwa suka ci gaba da tafiya haka za a samu fari,” wani manomi a wajen birnin Maiduguri, Malam Ibrahim Ali, ya shaida wa NAN.
Manoman da dama da su ma suka yi magana kan wannan lamari mai tada hankali, sun ce sun koma yin addu’a.
A halin da ake ciki, Majalisar Masarautar Borno ta fara jan hankalin jama’a domin gudanar da addu’o’in samun ruwan sama, wanda ake kira “Salatul Istisqa’a”.
Sanarwa daga Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar Garbai El-Kanemi, ya bukaci al’ummar Musulmi da su hallara a dandalin Ramat Square Maiduguri a yau Litinin domin yin addu’a.
Sanarwar mai dauke da sa hannun sakataren Shehu Malam Zannah-Umar Ali, ta bukaci al’ummar musulmi da su tashi tsaye ba tare da la’akari da shekaru, jinsi da matsayi domin gudanar da addu’a ta musamman ba.


