Manjo-Janar Bernard Onyeuko mai ritaya, wanda tsohon kakakin soji ne ya rasu.
Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon Daraktan, Operation Media Operations ya rasu ne a safiyar ranar Asabar bayan ya yi korafin yana jin sanyi kuma an garzaya da shi wani asibiti mai zaman kansa.
Da yake mayar da martani kan rasuwar, Garba Shehu, tsohon kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi addu’ar Allah ya sa Onyeuko ya huta.
“Karanta labarin mai ban tsoro cewa mun yi rashin abokinmu, tsohon kakakin soja, Manjo-Janar Bernard Onyeuko (rtd).
“Allah Madaukakin Sarki Ya ba wa ‘yan uwa hakurin jure rashin. RIP.” ya wallafa a shafinsa na Twitter.


