Wasu daga cikin maniyata aikin hajjin jihar Kano sama da dari 300 sun zargi hukumar jindadin alhazan jihar da yi musu ta leko ta koma kan tafiyarsu aikin hajjin bana.
Minyatan dai sun ce sun biya kudaden su na tafiya fiye da shekara guda, sannan har an gama tantance su, sai daga bisani bayan alhazan Kanon sun fara tafiya aka zo aka sanar da su cewa babu su a aikin hajjin na bana.
Maniyittan da suka yiwa ofishin alhazai na Kano tsinke sun ce ba za su amince da wannan tsarin na tauye mu su hakki ba.
Wata dattijuwa da ta fito daga Karamar hukumar Dawakin kudu ta ce sai da ta gama dukkan shirin tafiya har ma ta karbi jaka aka ce mata ta dawo
Abba Dambatta shine shugaban hukumar alhazai ta jihar Kano, ya ce babu hannun hukumarsa a wajen matsalar da suka fuskanta, don babu wanda ya saka kudin asusun da suka bayar
Sai dai duk kokarin da BBC ta yi don jin ta bakin ofishin hukumar ralhazai na Najeriya hakan ya ci tura, sakamakon rashin amsa kira wayar da dawo da amsar sakon da mu ka aikewa jami’ar hulda da jama’a na hukumar Hajiya Fatima Sanda Usara.
Wannan dai na zuwa ne kwana guda da fara tashin alhazan jihar Kano, wanda kimanin alhazai sama da dubu biyu ake sa ran za su isa kasa mai tsarki don yin aikin hajjin bana.
Ko a makonin da suka gabata sai da aka sami musayar kalamai tsakanin hukumar jin dadin alhazai a Kano da Kamfanin jirgin sama na Azman kan jigilar alhazan jihar da aka ce kamfanin zai yi tare da jirgin Max Air da Fly Nas mallakar kasar Saudiya.