fidelitybank

Maniyatan bana za su biya sama da Naira miliyan biyu – NAHCON

Date:

Hukumar kula da aikin hajji ta ƙasa NAHCON, ta sanar da cewa, maniyyata aikin hajjin bana za su biya kuɗi da ya kai naira miliyan biyu da dubu 890 a matsayin kuɗin kujera.

Shugaban hukumar Zikrullah Hassan, shi ya bayyan haka a yau Juma’a, inda ya ce, matsalar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya da kuma Saudiyya a matsayin abubuwan da suka janyo ƙaruwar kuɗin hajjin bana.

Hassan ya ce, farashin ya kai matakai takwas, inda jihohin Borno da Yobe suka kasance jihohi da za su biya kuɗi mafi ƙanƙanta yayin da Legas da Ogun za su biya kuɗi mafi girma da ya kai naira miliyan biyu da dubu 990.

Hakan ya faru ne sakamakon bambancin kuɗin jirgi da kuma kuɗin masaukai a Makka.

Maniyyatan jihohin arewacin ƙasar za su biya naira miliyan biyu da dubu dari tara da goma sha tara.

Jihohin kudancin kasar kuma su ma za su biya kusan miliyan uku.

Hassan ya ce abin da ya sa aka samu bambancin kuɗi shi ne yankin arewacin Najeriya ya fi kusa da Saudiyya a kan kudancin ƙasar, kuma irin masaukin da kowace jiha ke kama wa, shi zai nuna adadin kuɗin da za su biya.

Ya ce kamfanonin jiragen sama da aka amince su yi jigilar maniyyata daga jihohi sun haɗa da Air Peace da Azman da Fly Nas da Aero Contractors da kuma Max Air yayin da Arik Air da Value jet aka amince da su a matsayin jiragen haya masu zaman kansu.

leadership newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp