Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON, ta ce, aƙalla maniyyatan Najeriya 51,447 ne za su sauke farali a aikin Hajjin bana a ƙasar Saudiyya.
Shugaban hukumar, Malam Jalal Arabi, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar ranar Juma’a a Abuja.
Arabi ya ce hukumar na tsare-tsare wajen ganin ta gudanar da aikin Hajji cikin nasara, ko da kuwa za a fuskanci kalubale.
Ya nanata cewa Msulman Najeriya za su yi aikin Hajjin 2024 a adadin da babu wanda ya taɓa tunani.
“Shirye-shiryen Hajjin bana na ɗaya daga cikin mafi wahala da aka taɓa gani,” in ji shi.
Ya ce a baya, an samu lokaci mai yawa na yin shirin da ya kamata, amma a wannan karon, Saudiyya ba ta ba su isasshen lokaci ba.
Malam Arabi ya ce gwamnatin tarayya ta shiga taimaka ta hanyoyi da dama, musamman ma ɓullo da wasu tsare-tsare na tallafa wa hukumar domin tabbatar da cewa al’amura su tafi yadda ya dace.
Ma’aikatar aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta ware wa Najeriya kujeru 95,000 domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2024.