fidelitybank

Maniyata 25,702 na Najeriya na kasar Saudiyya – NAHCON

Date:

Ma’aikaar kula da aikin hajji ta kasa NAHCON, ta bayyana cewa an kwashe maniyyata aikin hajji daga jahohi 12 na ƙasar, waɗanda yawansu ya kai mutum 25,702.

Jihohin su ne Osun da Oyo da Adamawa da Filato da Ekiti Imo da Legas da Abiya kuma Edo.

Hukumar alhazan ta ce an kwashe wannan adadin ne bayan sawu 63 daga Najeriya zuwa Saudiyya a cikin kwana goma.

Kawo yanzu dai hukumar ta ce babu wata matsala da aka fuskanta tun bayan soma jigilar maniyyatan, inda a wannan shekarar hukumomin suka ce mutum 43,000 ne za su sauke farali a ƙasar ta Saudiyya domin gudanar da babbar ibadar ta Musulmai.

A ckin wata sanarwa da jami’in gudanarwar hukumar na ƙasa, Ibrahim Muhammad ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa matakan da hukumar ta ɗauka da ke kan tsari sun taimaka matuƙa inda jigilar maniyyatan da sauran ayukan kula da su a ƙasar ta Saudiyya ke tafiya cikin nasara.

An fara jigilar ne a ranar 9 ga wannan watan na Mayun 2025 inda kuma aka soma daga filin jirgin sama na birnin Owerri da ke jihar Imo a kudu maso gabashin Najeriya.

assu today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp