A Jamhuriyar Nijar kimanin maniyata sama da 2000 ne ba su samu tafiya ba duk kuwa da cewa sun samu biza.
Sai dai masana harakokin aikin Hajji da Umara na cewa matsalar ta kowane bangare ce ba ta bangare daya ba . Sai dai masu alhakin jigilar alhazan na cewa sun yi iya kokarin su wajen ganin sun kwashe daukacin maniyatan kafin cikar wa’adin.
Daga Yamai ga rahoton da Tchima Illa Issoufou ta aiko.