fidelitybank

Maniyaciyar jihar Kaduna ta rasu bayan ta dawo daga Arafat

Date:

Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON, ta tabbatar da rasuwar Hasiya Aminu, wata maniyaciyar jihar Kaduna.

Ta rasu ne a cikin barcin da take yi jim kadan, bayan ta dawo daga dutsen Arafat, kamar yadda makwabtanta a cikin tanti suka bayyana.

Dakta Usman Galadima, babban jami’in aiyuka, kuma shugaban ma’aikatan lafiya na kasa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) cewa, har yanzu ba a tantance dalilin mutuwar ta ba.

Ya ce, tuni aka sanar da iyalan ta rasuwarta kuma za a yi jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Usman shi ne mahajjaci na biyu da ya rasu a aikin Hajjin 2022.

Hajiya Aisha Ahmed daga Keffi a jihar Nasarawa ita ma ta rasu a makon jiya bayan gajeriyar rashin lafiya kuma an yi jana’izarta a Makkah.

Zaman Arafa a tsawon yini ya zama wajibi ga kowane mahajjaci ya cika domin yin aikin Hajji.

Alhazan Najeriya daga cikin sama da miliyan daya da ke aikin Hajjin shekarar 2022 a Arafat.

Arafat ita ce wurin da Annabi Muhammad ya gabatar da hudubarsa ta karshe a ranar Juma’a kafin rasuwarsa.

daily sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp