Jihar Legas ta rasa daya daga cikin maniyyacin ta aikin hajjin bana a kasar Saudiyya.
Marigayin mai suna Oloshogbo Isiaka Idris, ya rasu ne bayan ya dawo daga dawafi a Makkah.
A cewar wata sanarwa da mataimakin daraktan hulda da jama’a na hukumar jin dadin alhazai ta jihar Legas, Taofeek Lawal, sakataren hukumar Saheed Onipede ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa, marigayin mai shekaru 68 ya fito ne daga karamar hukumar Shomolu ta jihar.
Ya kuma rasu yana cin abincinsa bayan sallar isha’i.
Ko da yake ya ce, har yanzu ba a gano musabbabin mutuwar Idris a likitance ba, amma ba za a iya rasa nasaba da cutar hawan jinni ba.
Ya kara da cewa, an yi jana’izar marigayi Idris a Makkah bisa ka’idojin hukumomin Saudiyya, yayin da wani ma’aikacin hukumar Waheed Ololade Shonibare ya jagoranci wasu jami’an gwamnatin jihar da wasu alhazai wajen gudanar da sallar janaza ga mahajjata a Kabah.
Yayin da yake mika ta’aziyyar gwamnatin jihar ga ‘yan uwa da abokan arziki na marigayin, ya yi addu’ar A… ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma ba shi Aljanat Fridaos da kuma ladan aikin Hajji.
Sakataren hukumar ya kuma yi kira ga sauran maniyatan da su yi taka-tsan-tsan tare da kiyaye wuce gona da iri kafin a fara aikin hajji na bana.