Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Abuja (FCT-MPWB), ta shawarci maniyyatan 2024 da ke son zuwa kasar Saudiyya da su saka Naira miliyan 4.5 ga hukumar har sai an tantance ainihin kudin.
Mataimakin babban jami’in yada labarai na hukumar, Ahmad Saleh ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Juma’a.
Ya ce za a fara sayar da fom da rajistar aikin ne a ranar 25 ga Satumba.
Saleh ya bukaci mahajjata da su biya hukumar jin dadin alhazai ta Abuja, ta hanyar wani daftarin banki.
Ya bukace su da su gabatar da fasfo na kasa da kasa ingantacce, da kuma lambar shaidar kasa a wurin yin rajista a kowace karamar hukumar guda shida da ke FCT.
“Hukumar ba ta karɓar ajiyar kuɗi kuma ba ta yin rajista ta hanyar wakili.
“Hakanan za ta bi ka’idodin farkon zuwan farko,” in ji shi. (NAN)


