Manhajar bincike na Google, ya sanya sunan gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf a matsayin tsohon gwamnan jihar.
Yayin da, Wikipedia ya amince da Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin gwamnan jihar Kano.
Wikipedia ya wallafa su biyun a matsayin gwamnonin jihar Kano.
Wani bincike da aka yi a Google kan wanene Abba Kabir Yusuf ya samar, matsayin tsohon gwamna.
Ku tuna cewa kotun daukaka kara ta jihar Kano a ranar 20 ga watan Satumba a hukuncin da ta yanke ta soke zaben Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano tare da bayyana Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano na 2023.
Sai dai Abba Kabir Yusuf da NNPP sun sha alwashin kalubalantar hukuncin a kotun daukaka kara.
Sai dai an gano a ranar Asabar cewa Wikipedia ta sabunta shafinta na yanar gizo kwanaki uku da suka gabata inda ta amince da Abba Kabir Yusuf da Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin gwamnonin jihar Kano.
Wikipedia wani encyclopedia ne na kan layi kyauta wanda gungun masu sa kai suka rubuta kuma suke kiyaye su, waÉ—anda aka fi sani da Wikipedian, ta hanyar haÉ—in gwiwa a buÉ—e da kuma amfani da tsarin gyare-gyare na tushen wiki mai suna MediaWiki. In ji Solacebase.