Sadio Mane ne ya ci kwallonsa ta farko a gasar Bundesliga a lokacin da Bayern Munich ta bude sabon kamfen da ci 6-1 a Eintracht Frankfurt.
Kungiyar da ta lashe gasar Europa Frankfurt ta zama abokiyar hamayya ta farko ga zakarun, amma kungiyar Julian Nagelsmann ta kawar da su gefe cikin salo mai ban sha’awa.
Bayan da Bayern ta doke RB Leipzig da ci 5-3 a gasar DFL-Supercup a makon da ya gabata a wasansu na farko bayan ficewar Robert Lewandowski.
Joshua Kimmich, Benjamin Pavard, Jamal Musiala da Serge Gnabry Mane sun zura ƙwallaye a gasar.
A yau Asabar Borrussia Dortmund za ta kara da Bayer Leverkusen a gasar.


