Sadio Mane ya yi bankwana da takwarorinsa na Bayern Munich ranar Lahadi kafin ya koma Al Nassr, in ji Sky Germany.
Mane na shirin yin gwajin lafiya tare da Al Nassr a wannan makon.
Dan wasan na Senegal din zai rattaba hannu kan kwantiragin shekaru hudu na sama da Yuro miliyan 40 (£34.4m) da kulob din na Saudi Arabiya.
Mane dai ya koma Bayern Munich ne daga Liverpool a bara. Dan wasan gaba bai taka rawar gani ba a kakar wasa ta farko da zakarun Bundesliga.