A ranar Alhamis ne Manchester United ta nada Rene Hake da Ruud van Nistelrooy a matsayin mataimakan manajan kungiyar farko ta maza.
Kociyoyin biyu za su yi aiki a karkashin kocin Erik ten Hag har zuwa watan Yuni 2026.
Da yake mayar da martani, Ten Hag ya bayyana farin cikinsa, inda ya kara da cewa dukkan mutanen biyu za su kara wa ma’aikata dimbin kwarewa, ilimi da sabbin kuzari.
“Na yi farin ciki cewa Rene da Ruud sun amince su shiga aikinmu, tare da kara yawan kwarewa, ilimi da sabon makamashi ga ma’aikata,” in ji Ten Hag kamar yadda shafin yanar gizon Man United ya nakalto.
“Yanzu lokaci ne mai kyau don sabunta Æ™ungiyar masu horarwa yayin da muke neman haÉ“aka nasarorin da aka samu a cikin shekaru biyu da suka gabata da kuma matsawa zuwa mataki na gaba.”


