Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta gargadi Cristiano Ronaldo da cewa dole ne su ga canji a halayensa ko kuma su yi tunanin soke kwantiraginsa.
A cewar Sky Sports, wannan na zuwa ne bayan da Red Devils ta sha kashi da ci 4-0 a Brentford ranar Asabar.
Wannan ne karon farko da Ronaldo ya fara bugawa kungiyar bayan ya yi kokarin barin Old Trafford a yunkurin buga gasar zakarun Turai.
Sai dai dan wasan mai shekaru 37 ya kasa samun wata muhimmiyar gudunmawa a wasan.
Ronaldo ya kuma caccaki magoya bayan United bayan an tashi wasan kuma ya kutsa cikin ramin da ke cikin dakin da ake saka tufafi.
Ballon d’Or sau biyar ana alakanta shi da komawa Bayern Munich, Atletico Madrid, da Paris Saint-Germain, amma yunkurin ya kasa cimma ruwa.


