Dan wasan baya na Bayern Munich, Matthijs de Ligt, ya samu tayin kwantiragin shekaru biyar daga Manchester United.
A cewar Sky Germany, De Ligt yana sha’awar tafiya.
An kuma yi imanin cewa United ta fara tattaunawa da Bayern, don bincika yanayin yuwuwar yarjejeniyar.
Erik ten Hag, wanda ya yi aiki tare da De Ligt a Ajax, yana son mai tsaron baya a matsayin wani bangare na tawagarsa a Old Trafford a kakar wasa mai zuwa.
Bayern ta kimanta dan wasan mai shekaru 24 akan €50m (£42.4m) gami da add-ons.
United, duk da haka, ta ci gaba da zawarcin dan wasan bayan Ingila Jarrad Branthwaite amma za ta koma neman dan wasan ne kawai idan Everton na son sauka a farashin da take nema.