Manchester United ta sanar da cewa Antony ba zai koma kungiyar ba, bayan hutun wasanni na kasa da kasa sakamakon zargin cin zarafi.
Tsohuwar budurwar Antony, Gabriela Cavallin, ta yi ikirarin cewa dan wasan ya ci zarafinta sau hudu.
Wasu mata biyu a Brazil, Rayssa de Freitas da Ingrid Lana, sun kuma zargi dan wasan mai shekaru 23 da cin zarafi.
Brazil ta kori Antony a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da Bolivia, kuma United ma ta ja layi daya da shi.
“Man Utd ta amince da zargin da ake yi wa Antony. Zai jinkirta dawowar sa har sai wani lokaci domin magance wannan zargi.
“A matsayinmu na kulob muna yin Allah wadai da ayyukan tashin hankali da cin zarafi”.
A cikin sanarwar nasa, Antony ya ce: “Na amince da United ta dauki wani lokaci ba tare da na yi magana game da zargin da aka yi mini ba.
“Wannan shawara ce ta juna.
“Ina so in sake jaddada rashin laifi na daga abubuwan da ake zargina da su, zan ba ‘yan sanda cikakken hadin kai”.


