Manchester United ta kammala siyan dan wasan tsakiya na kasar Denmark Christian Eriksen a matsayin kyauta.
Tsohon dan wasan Ajax da Tottenham, Inter Milan da Brentford ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru uku a Old Trafford.
A farkon watan Yuli, Eriksen ya amince da ka’ida, domin sanya hannu a United bayan ɗan gajeren wa’adin kwantiraginsa a Brentford ya ƙare a watan Yuni.
Shi ne dan wasa na biyu da United ta saya a karkashin sabon koci, Erik ten Hag, bayan dan wasan baya na Netherlands Tyrell Malacia daga Feyenoord.