Manchester City ta doke Fulham tare da ɗarewa kan teburin Premier League, yayin da Haaland ya zura ƙwallo ta 50 a duka wasannin da ya buga wa City a kakar bana.
Haaland ya ci bugun fenareti a minti na uku da fara wasan, bayan da ka yi wa Alvarez ƙeta – ƙwallo da ta sa shi zama ɗan wasa na farko a gasar Premier da ya ci ƙwallo 50 a kaka ɗaya, tun bayan Tom ‘Pongo’ Waring da ya yi wannan bajinta a ƙungiyar Aston Villa a shekarar 1931.
Da wannan bajinta a yanzu ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Norway ya kamo tarihin bajintar Andy Cole da Alan Shearer suka kafa na cin ƙwallo 34 a gasar Premier a kaka guda.
Fulham ta samu damar farke kwallon a minti na 15, to sai dai a minti na 36 Alvarez ya sake saka City a gaba, bayan da ya buga wata ƙwallo daga tazarar yadi na 25, inda kuma aka tashi a haka.
Nasarar ta bai wa City damar ɗarewa kan teburin gasar Premier da zatarar maki guda tsakaninta da Arsenal yayin da Cityn ke da kwantan wasa.
Wannan shi ne karo na farko da City ta hau saman Arsenal a kan teburin gasar ta bana tun tsakiyar watan Fabrairu, yayin da take fatan lashe kofin Premier da na Zakarun Turai da kuma kofin FA duk a kakar wasa ta bana.