Manchester United na shirin siyan tsohon dan wasan baya na Chelsea Marcos Alonso yayin da take neman karfafa kungiyar kocinta Erik ten Hag a kasuwar musayar ‘yan wasa ta bazara.
Alonso a halin yanzu yana samuwa a matsayin wakili na kyauta bayan ya bar Barcelona a bazara bayan karewar kwantiraginsa.
A cewar The Mirror, Man United na son karfafa zabin dan wasan baya na hagu a wannan bazarar kuma ta sanya dan wasan mai shekaru 33 a cikin jerin ‘yan takara uku da za su taimaka wajen magance matsalolinsu a baya.
Alonso daya ne ake hari tare da David Hancko na Feyenoord da kuma Tyrick Mitchell na Crystal Palace.
Ana danganta Hancko da komawa Atletico Madrid, amma an ce yarjejeniyar ta ci tura, yayin da AC Milan kuma ta ce tana zawarcinsa.
Mitchell, a gefe guda, yana iya kasancewa a farashi mai rahusa ganin cewa ya shiga watanni 12 na ƙarshe na kwantiraginsa a Crystal Palace.


