Allah ya yiwa shugaban hukumar gudanarwa da tsaftar mahalli (REMASAB) ta Kano, Haruna Danzago rasuwa.
Majiyar ‘yan uwa ta ce ya rasu ne a safiyar ranar Alhamis a asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH) da ke Kano sakamakon rashin lafiya.
Danzago, ma’aikacin gwamnati ne, kuma dan siyasa mara tsoro, ya shahara da irin gudunmawar da yake bayarwa a harkokin siyasa a jihar Kano.
Gwamnan jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf ne ya nada shi a matsayin Manajan Daraktan REMASAB a ranar 5 ga Yuli, 2023.
Majiyoyi sun ce za a yi jana’izarsa a gidansa da ke Kurna Tudun Bojuwa, a Kano.