Ƙungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur ta OPEC ta ce, yawan man da Najeriya ke fitarwa zuwa kasuwannin duniya ya ƙaru da kashi 60.8 a rubu’i na uku na shekarar 2023.
Cikin rahoton wata-wata da ƙungiyar ta fitar ranar Talata, ta ce ”A cikin rubu’i na uku na shekarar 2023, adadin man da Najeriya ke fitarwa ya ƙaru da kashi 60.8, sannan wanda take shigarwa ya karu da kashi 47.7, abin da ya sa aka samu rarar naira biliyan 1,888.92 a tsakanin wannan lokacin”.
Rahoton ya kuma ce Najeriya ta samu ƙarin rarar naira biliyan 1,438 daga naira biliyan 7.2 da ta samu a watan Satumban 2022.
”A ƙarshen watan Janairun da ya gabata an farashin kudin ƙasar Naira ya karye, inda aka riƙa chanja kowace dala a kan naira 975 zuwa naira 1,424, lamarin da ka iya ƙara ta’azzara hauhawar farashi”, in ji sanarwar.
Yawan man da ƙasar ke fitarwa a halin yanzu ya yi ƙasa da abin da aka ƙiyasta a kasafin kuɗin ƙasar, wanda ya kiyasta fitar da gangar mai miliyan 1.78 a kowace rana, a kasafin kuɗin da ya dogara sosai kan sayar da man.