fidelitybank

Man fetur ya ragu a Najeriya sakamakon a na shanye shi

Date:

Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya, NMDPRA ta ce yawan man da ake amfani da shi a ƙasar a kowacce rana ya ragu zuwa lita miliyan 46.34, sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi.

Shugaban hukumar, Ahmed Farouk, ne ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki kan harkokin albarkatun man fetur da iskar gas a birnin Legas, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN ya ruwaito.

Ya ƙara da cewa raguwar ta kai kashi 35 cikin 100 idan aka kwatanta da lita miliyan 65 da ake amfani da shi a kowacce rana kafin cire tallafin man fetur ɗin.

Ahmed Farouk ya ce ”a watan Janairu fabrairu, an sha mai lita miliyan 62 a kowacce rana, yayin da aka sha lita miliyan 71.4 a kowace rana cikin watan Maris, sai Afiru da aka sha lita miliyan 67.7 a kowacce rana, sai watan Mayu da aka sha lita miliyan 49.5 a kowace rana, sai kuma watan Yuli da ake shan lita miliyan 46.3 a kowace rana”.

Shugaban hukumar ya kuma gode wa ‘yan kasuwar da suka nuna sha’awarsu wajen shigar da man fetur ƙasar daga kasuwannin duniya.

Ya kara da cewa kawo yanzu kamfanoni 56 ne suka nuna sha’awarsu wajen shigo da man fetr zuwa ƙasar, yayin da kamfanoni 10 suka zaku wajen fara shigo da man.

Ahmed Farouk ya ce yanzu haka kamfanoni uku sun fara shigo da man fetur ɗin daga ƙasashen waje.

assu today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp