Shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden na son yin wata ziyarar aiki zuwa Saudiyya, domin tattaunawa da Sarki Salman kan bukatar kasarsa na bunkasa yawan man fetur din da kasar da ke hakowa.
Wata mujallar siyasa ta Amurka mai suna Axios ce, ta wallafa labarin, ta na cewa nan da watan gobe shugaban Amurkan zai kai ziyarar yayin da Fadar White House, ke kokarin shawo kan rikicin karancin makamashi a duniya wanda yakin Rasha da Ukraine ya haifar.
Sai dai kakakin Fadar White House ta ce, kawo yanzu ba a bayyana ranar da zai kai ziyarar ba, ya na cewa “dukkan abubuwa da ake cewa hasashe ne kawai.”
Akwai wani rahoton da ke cewa jami’an gwamnatin Amurka da na Venezuela kan janye takunkumin da Amyurka ta kakaba wa Venezuelan. Wasu ‘yan majalisar Amurka na cewa Amurka na iya maye gurbin man fetur din da Amurka ke sayowa daga Rasha da na Venezuela. A cewar BBC.