Masu masana’antun na nuna matukar damuwa yayin da farashin man dizal ke ci gaba da hauhawa, inda ya kai Naira 1,275 a kowace lita a Legas, sannan ya haura Naira 1,300 a yankunan da ke wajen jihar.
Jaridar Daily trust ta ruwaito cewa wannan ƙarin farashin man dizal ya yi kamari a wasu yankuna, inda farashin litar ya kai Naira 1,270 a jihar Kano, wanda ya ma fi girma a wajen birnin.
Tabarbarewar farashin man dizal na haifar da fargaba a tsakanin masu ruwa da tsaki domin ya zama babbar barazana ga al’ummar kasar da tuni ke kokawa da hauhawar farashin kayayyaki.