Babbar kotun Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce, mamayar Isra’ila a yankunan Falasdinawa ta saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.
Kotun ta duniya ta yi umarni ga Isra’ila ta gaggauta dakatar da ayyukanta na mamayar yankunan Falasdinawa a Gabar Yamma da Kogin Jordan da kuma Gabashin Kudu, ayyukan da ta kira “haramtattu.”
A martaninsa, Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana matakin na kotu a matsayin “ƙarya.”
Duk da cewa wannan matsayar ta kotun ICJ ba doka ba ce, amma tana da tasiri sosai a siyasance. Karon farko kenan da kotun ta bayyana matsayarta game da halaccin mamayar Isra’ila a yankunan Falasdinawa tsawon shekara 57.
Kotun ta ICJ da ke da shalkwata a Hague kasar Netherlands, tun a bara take nazari kan batun bisa umarnin babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya.