Hukumar da ke yaki da yi wa tattalin arziki ta’annati ta kasa, EFCC ta sanar da samun nasara a kotu, bayan da aka yanke wa, Aisha Wakil, da aka fi sani da Mama Boko Haram, da wasu mutum biyu daurin shekara biyar a gidan yari.
Mai sharia Aisha Kumaliya ta babbar kotun jiha a Maiduguri ta kama Aisha Wakil, da Tahiru Sai’du da kuma Prince Lawal Shoyode da laifin almundahanar naira miliyan 71,400,000.
Daurin kuma zai kasance ba tare da damar biyan tara ba a cewar mai shariar.
Tun a watan Satumban 2020 ne aka sake gurfanar da wadanda ake tuhumar a gaban kotu bisa zarge-zarge biyu, na almundahanar ta sama da naira miliyan 71.