Gwamnatin mulkin soji a Mali ta ce, ta hana sabbin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da za a kara aikawa cikin kasar saboda dalilai na tsaro.
Matakin na zuwa ne, bayan da gwamnatin kasar ta kama sojojin kasar Ivory -Coast 49 a lokacin da suka shiga kasar, inda ta yi zargin cewa sojojin haya ne.
Amma Jami’an Ivory – Coast sun ce sojojin sun je Mali ne domin aiki da dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar. In ji BCC.
Gwamnatin mulkin sojin Mali, da ke kokarin dakile hare-haren masu ikirarin jihadi, ta ce ba a sanar wa ma’aikatar harkokin wajenta ba, kafin aike wa da dakarun cikin kasar.