Ƙasar Mali ta ce za ta tura tawagar ta haɗin guiwa da Burkina Faso domin jaddada goyon bayan su ga sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar din.
Sanarwa na zuwa ne bayan da Sojin na Nijar suka yi watsi da umarnin Ecowas na mayar da mulki ga hamɓararren shugaban bisa karagar mulkin ƙasar.
Sojojin Nijar sun sanar da rufe sararin samaniyar su da iyakokin ƙasar, sun kuma ce a shirye suke wajen kare ƙasarsu.
Kawunan ƙasashen ƙungiyar Ecowas ya rabu kan ɗauka matakin soji ga Nijar, koda yake shine mataki na ƙarshe da ƙungiyar tace za ta ɗauka.
Najeriya da Ivory Coast na kan gaba wajen jaddada buƙatar mayar da shugaba Bazoum bisa shugabancin ƙasar.
Sai dai shugabannin mulkin soji na ƙasashen Mali da Burkina Faso sun nuna goyon bayan su ga Sojojin Nijar, sun kuma ce zasu shigar masu faɗa mudin Ecowas ta kai wa Nijar hari. In ji BBC.