fidelitybank

Mali da Burkina Faso sun aika wa Nijar jiragen yaƙi

Date:

Ƙasashen Mali da Burkina Faso sun aika wa Nijar jiragen yaƙi ɗai-ɗai don nuna goyon bayansu ga sojojin mulkin ƙasar da suka yi juyin mulki a watan Yuli.

Wani rahoto da kafar talabijin ɗin RTN ta gwamnatin ƙasar ta yaɗa ranar Juma’a ya ce ƙasashen biyu sun fara cika alƙawarin da suka ɗauka na taimaka wa Nijar kare kanta daga harin da Ecowas ke shirin kai mata don dawo da mulkin farar hula.

“Mali da Burkina Faso sun fara ɗaukar matakan cika alƙawari ta hanyar aiko da jirage don kare duk wani hari a kan Nijar,” in ji rahoton.

An bayyana cewa jiragen na kai hari ne ƙirar Super Tucano. In ji BBC.

A jiya Juma’a hafsoshin tsaro na ƙungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma wato Ecowas suka ce sun saka ranar da za su afka wa Nijar don mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan mulki.

Sai dai sun ce ba za su faɗi ranar ba, kuma za a ci gaba da yunƙurin shawo kan lamarin ta hanyar difilomasiyya.

yola news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp