Gwamnatin Malaysia na shirin soke hukuncin ɗaurin rai da rai da kuma na kisa kan laifuka shida, domin yin garanbawul ga tsarin shari’ar ƙasar.
Dokar da aka gabatar za ta bai wa alkalai ikon yanke hukunci kan yadda za a hukunta waɗanda aka samu da laifuka daban-daban, kama daga safarar miyagun kwayoyi zuwa kisa.
Ministar shari’a da sake fasalin hukumomin Malaysia, Azalina Usman Saeed, ta shaida wa majalisar dattijai a birnin Kuala Lumpur cewa za a gabatar da kudurin doka kan sauye-sauyen da ake shirin gabatarwa a majalisar dokokin ƙasar a ranar 27 ga watan Maris.
Dokokin Malaysia na yanzu sun tanadi hukuncin kisa kan laifuka 34 da suka haɗa da kisan kai da fataucin miyagun kwayoyi da kuma ta’addanci a ƙasar da ke kudu maso gabashin Asiya.
Mai magana da yawun ma’aikatar shari’a da sake fasalin hukumomin Malaysia, ya ce a cikin sabbin shawarwarin, hukuncin kisa ba zai sake shafar laifukan da suka shafi safarar bindigog da kera makamai da kuma yin garkuwa da mutane ba, inda za a yanke musu hukuncin ɗaurin shekaru arba’in a gidan yari ko bulala maimakon kisa.
Hukuncin kisa zai kasance zaɓi ne ga alkalai yayin da ake fuskantar wasu laifuffuka da suka haɗa da ta’addanci da kuma kai hari ga masarautar Malaysia.