Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, a ranar Litinin ya gargadi shugaban kasa Bola Tinubu cewa dala za ta iya kaiwa Naira 1,700, sannan za a sayar da buhun shinkafa kan N90,000.
Ya ce kamata ya yi Tinubu ya daure wa matsalar tattalin arziki da ke tafe matukar ba a samar da mafita don kawo karshen rudanin da kasar nan ke fama da shi ba.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Osho Oluwatosin ya sanya wa hannu, Primate Ayodele ya bayyana cewa idan shugaban kasar bai yi abin da ake bukata ba, tattalin arzikin Najeriya ba zai daidaita ba har zuwa 2026.
Ya shawarci gwamnati da ta samar da tsaro, ta durkusar da farashin kayan masarufi, samar da isasshiyar wutar lantarki da inganta kayayyakin cikin gida domin a yi karo da dala da kuma saukaka wa ‘yan Najeriya nauyi.
Bawan Allah ya bayyana cewa matakan da gwamnatin ta dauka kawo yanzu ba za su taimaki kasar nan ba illa kara hauhawar farashin kayayyaki.
A cewar Ayodele: “Idan gwamnatin Tinubu ba ta yi abin da ake bukata ba, tattalin arzikin ba zai daidaita ba har zuwa 2026.
“Suna bukatar samar da tsaro, rage farashin kayayyakin abinci, samar da isasshiyar wutar lantarki da inganta kayayyakin cikin gida. Wannan zai taimaka wa gwamnati kuma zai lalata dala.
‘’Duk wadannan matakan da suke dauka ba za su yi tasiri ba; kawai zai haifar da hauhawar farashin kayayyaki. Idan ba su yi abin da ya dace ba Najeriya za ta sayi dala kan Naira 1,700, buhun shinkafa zai kai Naira 90,000 kuma zai kashe tattalin arzikin kasa. Da alama ba su da ra’ayoyin ba za su taimaka lamarin ba.”