fidelitybank

Malamin addini Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya rasu

Date:

Allah yayiwa fitaccen malamin addinin musulunci kuma babban limamin masallacin juma’a na Dutsen Tanshi, Dr. Idris Abdulaziz rasuwa bayan doguwar jinya da ba’a bayyana ba.

Marigayin ya rasu ne a daren ranar Alhamis, inda ya bar al’ummar Bauchi da sauran kasashen duniya cikin alhinin rashin wani babban malamin addini.

Za’ayi Sallar Jana’izar Dr. Abdulaziz a Bauchi da misalin karfe 10:00 na safe ranar Juma’a.

Dokta Abdulaziz, wanda ya yi fice wajen fafutukar tabbatar da adalci da sadaukar da kai ga addininsa, ya shiga takaddamar shari’a da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, tun a shekarar 2022. Yana fuskantar shari’a kan zargin bata masa suna, kuma a wani lokaci rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta bayyana cewa tana neman sa a gaban kotu.

Duk da wannan cece-kuce, Dr. Abdulaziz ya ci gaba da zama mutum mai daraja, wanda ya jawo sha’awar wa’azi da jajircewarsa kan al’amuran al’umma.

Labarin rasuwarsa ya haifar da cika bakin ciki da jinjina daga mabiya da masu goyon bayansa a shafukan sada zumunta, inda da yawa ke bayyana shi a matsayin jajirtacce kuma ba kakkautawa a cikin al’umma.

Duk da cewa har yanzu ba a bayyana cikakken bayani game da rashin lafiyarsa da rasuwarsa ba, babu shakka rasuwarsa ta haifar da da mai ido a fagen addini a jihar Bauchi.

daily post news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp