Gwamna Hope Uzodimma, ya shaidawa malaman makarantun firamare a jihar Imo cewa, ya yi tarayya da irin kalubalen da suke fuskanta wajen gudanar da ayyukansu, inda ya ba su tabbacin cewa, tare za su kawar da matsalolin.
Gwamnan ya yi magana ne a karshen mako a wani taro da ya yi da shugabannin makarantun firamare da malamansu da ma’aikatan hukumar ilimin matakin farko na jihar, a dandalin Rear Admiral Ndubuisi Kanu, Owerri, domin nemo bakin zaren warware matsalolin da suka addabi fannin.
A cewar babban sakataren yada labarai kuma mai baiwa gwamna shawara kan harkokin yada labarai, Oguwike Nwachuku, taron ya kuma kasance wata dama ce ga malamai da ma’aikatan IMSUBEB na jihar wajen gudanar da bayanansu da tantancewa ta jiki, domin baiwa gwamnati damar aiwatar da ingantaccen biyan albashi. karin albashi, karin girma da tsarin jin dadin jama’a ga malaman firamare.